Fursunoni Masu Daurin Rai Da Rai Za Su Yi Digirin Digirgir A Jami’ar NOUN

Get in here, start and or make contribution to interesting gist
LadyB
Posts: 381
Joined: Sun Nov 05, 2017 7:32 pm
Contact:

Fursunoni Masu Daurin Rai Da Rai Za Su Yi Digirin Digirgir A Jami’ar NOUN

Postby LadyB » Fri Apr 20, 2018 5:05 pm

Daga Idris Aliyu Daudawa Wasu fursunoni guda biyu da ke zaman daurin rai da rai a Nijeriya, Tunwashe Kabiru da Oladipupo Moshood, sun kammala digiri na biyu (da a ke kira Masters), inda a ranar Larabar da ta gabata su ka amshi takardun shaidarsu daga Budaddiyar Jami’ar Nijeriya, National Open Unibersity of Nijeriya (NOUN).

Shugaban jami’ar ta NOUN, Farfesa Abdalla Uba Adamu, ne ya mika mu su takardun shaidar digirin nasu a gidan yarin Kirikiri da ke Lagos a ziyarar da ya kai ta gani da ido bisa kasancewar gidan yarin a matsayin wata cibiya ta karatu na tafi-da-gidanka. Haka nan ma wani wanda ke zaman gidan kurkukun na Kirikiri, Mr Alegbe Afolabi, ya amshi takardar shaidar digirinsa na farko.

Wannan abin tarihi da ya faru ya sanya a hatta shugaban gandurobobi na kasa, Alhaji Jafaru Ahmed, da sauran wasu manyan jami’ai na hukumomin jama’an tsaro da kuma jami’ar sun halarci taron mika wa fursunoni satifiket nasu. Shi dai Tunwashe ya samu digiri na biyu a kan harkar gudanar da kasuwanci (Business Administration), yayin da shi kuma Moshood ya karanci bangaren zaman lafiya da warware sabani (Peace Studies and Conflict Resolution).

Don haka tuni Farfesa Abdalla ya yi mu su rijista, domin cigaba da karatunsu na digiri na uku, wato digirin-digirgir (PhD). Su wadanda su ka kammala karatun jami’ar su na daga cikin dalibai 5,976 na jami’ar da su ka hada da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, wanda a watan Janairu ne a ka yaye shi a wani bikin yaye dalibai wanda a ka yi a Abuja. Tunwashe, wanda a ka yanke ma shi hukuncin daurin rai da rai kuma ya yi shekaru goma a tsare, cewa ya yi, ya na mai imani da ikon Allah watarana zai iya kasancewa a fitar da shi daga gidan Kurkukun.

Ya kuma kara bayanin cewar, shi ya na tsammani kwakwalwarsa ba za ta iya daukar karatu yanzu ba, amma kuma sai ga maganar jami’ar NOUN, wacce ta bada damar yin karatun jami’a kyauta, ya na mai cewa, idan ba ta wannan hanyar ba da wahala ya yi cimma wannan nasara a rayuwarsa. Tunwashe ya ci gaba da cewa, “yanzu cikin ikon Allah ni ma Ina da nawa ilimin wanda zan y i alfahari da shi da kuma canza hali na wajen koyon sabuwar rayuwa da kuma mu’amala da al’umma. Ko shakka babu ni ma ban fidda tsammanin Allah zai yi na shi ikon a fitar da ni ba, don na bada gudunwata wajen gina kasata Nijeriya.”

Ya yi kira da jami’ar da ta kara samar da wasu abubuwan da a ke bukata wajen taimakawa yin karatun, saboda yin haka zai sa su dalibai su kara maida himmar karatun. Shi ma da ya ke nashi jawabin, Mataimakin Jami’ar Shugaban Jami’ar Mai Cikakken Iko, Farfesa Abdalla ya bayyana cewar ita jami’ar ta na ba wa ’yan fursuna wadanda su ka cdancanci su yi karatun jami’a dama kyauta ne daga digiri na farko har zuwa digirin digirgir a kuma fannoni daban daban, saboda a samu damar yin karatun jami’a.”

Ya kara jaddada bayanin cewa, akwai dalibai 420 wadanda fursunoni ne da ke karatun jami’ar a bangarori daban-daban, wadanda su na karatunsu ne yadda su ka tsara wa kansu ba kuma wasu ayyukan cikin aji wadanda za su damu dalibai. Abdalla ya bada tabbacin cewar jami’ar za ta ci gaba da ganin duk wani fursuna wanda ya cancanci karatun jami’a, sun yi amfani da damar da ita jami’ar ta bada, su kara wa kansu damar da ta samu, saboda idan sun kammala wa’adinsu na zaman gidan kurkuku, za su samu damar yin kyakkyawar rayuwa, domin ilmin da su ke da shi.Source


Stay informed when you download our app
https://play.google.com/store/apps/deta ... m.nounitesWho is online

Users browsing this forum: No registered users and 2 guests